Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin sama da N1trn

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 da ya kai Naira tiriliyan ɗaya da biliyan ɗari takwas ga ƴan majalisar dokoki guda biyar don tattaunawa da amincewa.
Fubara ya bayyana cewa kasafin kudin na shekarar mai zuwa zai mai da hankali wajen samar da ci gaba mai ɗorewa, inganta tattalin arzikin jihar, da kuma kyautata rayuwar al’ummar jihar.
A cewarsa, an ware fiye da Naira biliyan 30 don fannin noma, yayin da Naira biliyan 63 za su tafi kan harkokin ilimi, sai kuma Naira biliyan 97 da aka ware don fannin kiwon lafiya.
Kasafin kudin bana ya zarce na bara, wanda aka gabatar da Naira biliyan 800 a matsayin kasafin kudin shekarar 2024.
Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin sama da N1trn
Comments
Post a Comment