Kungiyar darikar kadiriyya ta kafa gidan rediyonta

Kungiyar Darikar Kadiriyya ta kasa reshen jihar Kano, ta kaddamar da bude kafar Radio mai zaman kanta ta farko a nan jihar Kano mai suna “Kadiriyya Radio Nigeria”da nufin yada al’amuran da suka shafi koyarwar addinin Musulunci.

Malam Ibrahim Isah Abdullahi Makwarari, wanda ya jagoranci kaddamar da bude tashar a yau, yace tashar za ta mayar da hankali wajen bayar da gudunmawar koyarwar addinin Musulunci.

Malam Ibrahim Makwarari wanda kuma shi ne shugaban Rabida Muhammaddiyya, ya kara da cewa samar da kafar zai sake fito da wasu hanyoyin isar da koyarwar addinin Musulunci, baya ga fito kokarin Darikar Kadiriyya na inganta harkokin koyo da koyarwa.

A nasa jawabin Malam Kamalu Adamu Kamaluddin, malami a kwalejin ilimi ta Sa’adu Rimi ya ce Akwai bukatar al’umma su bawa kafar gudunmawar da zata kawo sauyi a tsakanin al’umma.

kafar mai suna “Kadiriyya Radio Nigeria” wadda kai tsaye zata rika yada shirye-shirye a kafar Internet, za ta mayar da hankali wajen koyarwar addinin Musulunci da al’amuran da suka shafi yau da kullum

Kungiyar darikar kadiriyya ta kafa gidan rediyonta



Comments

Popular posts from this blog

Ortom reacts to criticisms of Gov Alia’s Benue State Civil Protection Guards

EPL: Salah overtakes Thierry Henry in all-time top goalscorer chart

Food security: Gov Zulum advocates large-scale irrigation farming in Lake Chad region